Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu
Shi ne mutum na farko ɗan asalin Jihar Katsina da ya samu muƙamin Farfesa a fannin harshen Larabci.
Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa.
Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci.
- Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani
- Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja
Marigayi Shehin Malami a Sashen Harshen Larabci na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina, inda a nan ya samu matsayin Farfesa.
Ya kasance Shugaban Sashen Larabci (HOD) na Jami’ar na farko tun da aka kirkiro ta a shekarar 2006, inda ya yi wa’adi biyu na tsawon shekara goma zuwa 2016.
Shi ne mutum na farko ɗan asalin Jihar Katsina da ya samu muƙamin Farfesa a fannin harshen Larabci.
Haka kuma yana daga cikin malaman da suka ƙaddamar da Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Ka Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a Jihar Katsina.
An haife shi a ranar 15 ga Fabrairu, 1953 unguwar Adoro da ke garin Katsina, kuma ya rasu yana da shekara 72, ya bar ’ya’ya 10 da jikoki 32.