Mahaifin Mario Balotelli ya rasu
A karshen makon jiya ne aka samu labarin rasuwar Francisco Balotelli mahaifin shahararren dan kwallon Italiya da yanzu haka yake buga wa kulob din Liberpool na Ingila kwallo Mario Balotelli. Labarin ya bazu ne bayan kulob din Liberpool ya fara yin atisaye a shirye-shiryen fara balaguro don tunkakar kakar wasa ta bana, amma sai aka […]
A karshen makon jiya ne aka samu labarin rasuwar Francisco Balotelli mahaifin shahararren dan kwallon Italiya da yanzu haka yake buga wa kulob din Liberpool na Ingila kwallo Mario Balotelli.
Labarin ya bazu ne bayan kulob din Liberpool ya fara yin atisaye a shirye-shiryen fara balaguro don tunkakar kakar wasa ta bana, amma sai aka ga babu Mario Balotelli a cikin ’yan kwallon da ke yin atisayen. Da aka yi bincike ne sai aka gano kulob din ne ya ba shi hutu don ya tafi Italiya akan rasuwar mutumin da ya rike shi tun yana dan karami a matsayin mahaifinsa watau Francisco Balotellio wanda Allah Ya yi wa rasuwa a karshen makon jiya.
A wata sanarwa da dan kwallon ya fitar a shafin abota na facebook, inda yake da magoya baya kimanin miliyan 10, ya gode wa daukacin magoya bayansa da suka aika masa sakonnin ta’aziyya.
Balotelli, mai kimanin shekara 24, an haife shi ne a Ghana a shekarar 1990. Kuma ainihin mahaifansa ana musu lakabi ne da iyalan Barwuah (Barwuah Family).
An ce ainihin iyayensa sun yi kaura zuwa Italiya ne tun Balotelli yana dan shekara 2 zuwa uku inda da isarsu kasar sai suka bar shi a gidan kula da marayu da marasa galihu ba tare da sun sake waiwayarsa ba a wani dalili na kashin kansu. A can ne Francisco Balotelli ya gan shi kuma jininsa ya hadu da Mario inda daga nan ya nemi izinin gwamnatin Italiya ta amince masa ya mayar da shi gidansa don ya cigaba da daukar dawainiyarsa. Tun daga wancan lokaci Mario ya taso a gidan attajiri Francisco kuma dalili kenan da dan kwallon ya mayar da sunan mahaifinsa ya koma Balotelli maimakon Mario Barwuah. Amma ita yayarsa mai suna Abgigail da yake ta taso ne a gaban iyayenta na ainihi ana kiranta ne Abigail Barwuah.
Ana sa ran Balotelli zai hadu da takwarorinsa ’yan kwallon Liberpool ne a gobe don cigaba da tunkarar kakar wasa ta bana, inda ake sa ran kulob din zai yi balaguro zuwa kasashen Asiya da na Austireliya don yin wasannin sada zumunta kafin a fara gasar rukunin firimiya na Ingila a ranar 8 ga watan gobe.