Mahaifin Rahama Sadau ya rasu

Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ne a garin Kaduna.

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu

Mahaifin fitacciyar jarumar nan a masan’antar Kannywood, Rahama Sadau, ya riga mu gidan gaskiya.

Jarumar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook tana mai cewa “Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa…” sannan ta ɗora wani hoto da aka rubuta Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un har sau uku a ƙarƙashin saƙon.

Shi ma abokin sana’arta, Ali Nuhu, a saƙon da ya wallafa mai ɗauke da hoton Rahama tare da mahaifinta, ya sake tabbatar da rasuwar.

Bayanai sun ce Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ne a garin Kaduna, inda nan gaba kaɗan za a yi masa jana’iza.