Mahaifin Sam Nda-Isaiah ya rasu
Mahaifin mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Sam Nda-Isaiah, wato Baba Clement Ndanusa Isaiah ya rasu yana da shekara 80 a duniya. Wata sanarwa daga Bashir Ahmad Mataimaki na Musamman kan harkokin watsa labarai (Hausa) na Sam Nda-Isaiah ta ce Mista Ndanusa Isaiah, ya rasu ne cikin daren a ranar […]
Mahaifin mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Sam Nda-Isaiah, wato Baba Clement Ndanusa Isaiah ya rasu yana da shekara 80 a duniya.
Wata sanarwa daga Bashir Ahmad Mataimaki na Musamman kan harkokin watsa labarai (Hausa) na Sam Nda-Isaiah ta ce Mista Ndanusa Isaiah, ya rasu ne cikin daren a ranar Talatar da ta gabata, a gidansa da ke garin Kaduna bayan gajeruwar jinya. Ya rasu ya bar mata da ’ya’ya tara da jikoki da dama.
Marigayin kwararren dan jarida ne da ya yi aiki a gidajen jaridu da dama da suka hada da kamfanin The Nigerian Citizen da Gaskiya Corporation, Zariya. Daga nan ne ya koma jaridar The Mail, sai kuma jaridar Northern People’s Congress a Jihar Kano. Yana daga cikin ma’aikatan farko na kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo a 1966, inda ya rike manyan mukamai da dama.
Ya rike Editan Wasanni da Editan Labarai, zuwa Mataimakin Edita da kuma Editan jaridar New Nigerian (yankin Arewa).
A Jamhuriya ta Biyu, ya yi aiki da jaridar The Triumph, mallakin gwamnatin Jihar Kano, inda ya rike mukamin Manajan Edita, a wasu lokutan kuma Manajan Darakta.
A 1983 ne Gwamnan Jihar Filato a lokacin Solomon Lar ta nada Baba Ndanusa Isaiah, Manajan Daraktan jaridar Standard da ke Jos, sai dai kafin sanar da fara aikin nasa sai aka rushe Jamhuriya ta Biyu.
Cikin wani dan takaitaccen bayani kan rasuwar mahaifinsa, Mista Sam Nda-Isaiah, ya ce duk da iyalan na cikin bakin cikin rashin, amma mahaifinsu ya rayu rayuwar da ba za a taba mantawa da shi ba.
A nan gaba ne, iyalan mamacin za su sanar da ranar da za a gudanar da bikin binne shi.