Mahaifin Sheikh Al-Sudais ya rasu
Mahaifin babban Limamin Masallaci mai alfarma da ke birnin Makkah, kuma shugaban manyan masallatan Makkah da Madina, Sheikh AbdurRahaman Al-Sudais, ya rasu. Marigayin mai suna Sheikh Abdulaziz Al-Sudais, an binne shi ne a makabartar Al-Adl da ke Makkah, bayan sallar Asuba, a ranar Alhamis din da ta gabataSheikh Abdullah Al-Johani, Limamin Masallacin Makka, shi ya […]
Mahaifin babban Limamin Masallaci mai alfarma da ke birnin Makkah, kuma shugaban manyan masallatan Makkah da Madina, Sheikh AbdurRahaman Al-Sudais, ya rasu. Marigayin mai suna Sheikh Abdulaziz Al-Sudais, an binne shi ne a makabartar Al-Adl da ke Makkah, bayan sallar Asuba, a ranar Alhamis din da ta gabata
Sheikh Abdullah Al-Johani, Limamin Masallacin Makka, shi ya jagoranci salalr jana’izar, wadda dimbin malaman addini da jami’an gwamnati da malaman makaranta da daliban Jami’atu Umm Al-kura, tare da dimbin mahajjata da suka zo umra, sun halarci jana’izar.
Marigayi Sheikh Abdulaziz, shi ma babban malamin addini ne kafin rasuwarsa, ya kuma rasu a asibitin Sarki Abdullah, a ranar Larabar makon jiya. Jaridun Okaz da Saudi gazette duk sun ruwaito labarin rasuwar mamaci, har zuwa kan yadda aka yi jana’izarsa.
Shi kuwa gidan talabijin na Aljazeera, kuskure ya tafka, inda ya baza wa duniya cewa, shugaban limaman Makkah da Madina ne ya rasu. Daga baya Aljazeera ta roki afuwar masu kallo, inda daga bisani ta bayyana rasuwar mahaifin Sheikh AbdurRahaman Al-Sudais, mai suna Sheikh AbdulAziz Al-Sudais.