Mahaifin tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya rasu

Ya rasu yana da shekara 93 ya bar ’ya’ya 19, ciki har da Sanata Kwankwaso

Mahaifin tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya rasu
Allah Ya yi wa Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso rasuwa.

Ya rasu da daren ranar Juma’a, 25 ga watan Disambar 2020 yana da shekaru 93 a duniya.

Sanata Kwankwaso ne ya tabbatar da rasuwar ta bakin babban mai taimaka masa kan harkokin cikin gida, Muhammad Inuwa Ali.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Saleh Kwankwaso shi ne Hakimin Madobi kuma Makaman Karaye, Dan Majalisar Sarki kuma daya daga cikin Masu Zabar Sarki a Masarautar Karaye ta Jihar Kano.

Alhaji Saleh Kwankwaso ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

Marigayin ya zama Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano na farko lokacin da marigayi Sarkin Kano Alhaji Dokta Ado Bayero ya nada shi a shekarar 2000.

Sarkin Karaye, Alhaji Dokta Ibrahim Abubkar II, ya nada Marigayin a matsayin Makaman Karaye kuma babban dan Majalisar Sarki, daya daga cikin Masu Zabar Sarki a Masarautar Karaye a watan Nuwambar 2020.

Hakan ya biyo bayan samar da karin masarautu hudu a Jihar Kano da Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya yi a watan Mayun 2019, ciki har da ta Karayen.

Sanarwar ta ce za a yi masa Sallar Jana’iza a gidan tsohon gwamnan da ke kan titin Miller Road a Kano da misalin karfe uku na yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.