Mahaifin yaron da ya boye a tayar jirgi daga Benin Zuwa Legas ya bayyana

Mahaifin yaron da ya buya a tayar jirgin sama, Daniel Oikhena, ya bayyana, bayan da Jami’an tsaron asiri na DSS suka mika yaron hannun ma’aikatar kula da harkokin mata. Mahaifin ya bayyana ne a lokacin da aka yi wata ganawa da iyayen yaron ga Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole.Mahaifin yaron Mista Osaigbobo Oikhena, direba ne […]

Mahaifin yaron da ya boye a tayar jirgi daga Benin Zuwa Legas ya bayyana

Yaro Daniel da ya buya a tayar jirgin samaMahaifin yaron da ya buya a tayar jirgin sama, Daniel Oikhena, ya bayyana, bayan da Jami’an tsaron asiri na DSS suka mika yaron hannun ma’aikatar kula da harkokin mata. Mahaifin ya bayyana ne a lokacin da aka yi wata ganawa da iyayen yaron ga Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole.
Mahaifin yaron Mista Osaigbobo Oikhena, direba ne dan shekara 44, ya bayyana wa manema labarai cewa, sabanin yadda ake ta bazawa cewa a shi da lafiya, a hakikanin gaskiya ba sa tare da uwar yaron, don haka kowa na zaune a wuri daban, a sanadiyyar sabanin da suka samu da matarsa. Ya ce matarsa taki yarda ta zauna a wurin da zai iya biyan haya. Don haka shekara daya da ta gabata ya bar gidan, ya koma inda zai iya biyan haya.
“Na zo nan ne don in sanar da duniya ni ne mahaifin Daniel. Da farko da na samu labarin, na yi tsammanin an sace dana ne. Sai matata ta ce kada in damu, idan al’amura suka saisaita za ta kirawo ni, Ban taba mafarkin zuwa Amurka ba, kuma ban auri wata matar ba. Matata ta ki bai wa jami’an tsaron asiri na DSS lambar wayata a lokacin da suka bukaceta,” inji shi.
Mista Osaigbobo, wanda ke zaune a Siluko Road, ya bayana cewa: Ina biyan kudin makarantar ’ya’yana da kudin abincinsu a kodayaushe, sabanin yadda ake yayatawa wai na gudu na bar matata da ’ya’yana.” Ya kuma zargi matarsa da yi wa duniya nunin cewa tamkar ba shi da rai.
Wata kungiya da ake yi wa lakabi da De RAUFS, ta bayyana a gidan Gwamnatin Jihar Edo, inda ta tabbatar wa Daniel da tallafin karatu, har zuwa jami’a. Shugaban lauyoyin kungiyar  ta De RAUFS, Yinka Muyiwa ya tabbatar da aniyar kungiyarsu na bayar da tallafin karatu ga Daniel har zuwa jami’a.
Mahaifiyarsa ta bayyana cewa tana jiran ma’aikatar harkokin mata ta mika shi hannun iyayensa.