Mahaifin ’ya’ya 19 ya sa wa jaririnsa suna ‘Ya Isa Haka’
Da a ce na san haka zata faru, da ban haifi ’ya’ya da yawa ba.
Wani magidanci mai suna Zeher Gezer mai mata biyu da ’ya’ya 19, ya rada wa jaririnsa na baya-bayan nan suna Yeter, wato ‘Ya Isa’ don nuna haihuwar ta isa haka.
Zeher Gezer wanda yake birnin Diyarbakir a kudu maso gabashin kasar Turkiyya, ya ce, shi da matansa duk suna kaunar ’ya’yansu kuma suna kokarin ciyar su.
- An ceto jaririn da aka sayar mako daya da haihuwarsa
- Saboda rashin haihuwa miji ya cinna wa matarsa wuta
Sanadiyyar bullar annobar Coronavirus Zeher ya kasance cikin mawuyacin hali kan yadda zai nemi aikin da zai ciyar da iyalansa.
A kasar Turkiyya an haramta auren mace fiye da daya, don haka magidancin ya auri matarsa ta biyu ce kamar yadda addini ya ba shi dama, amma ba a yi rajistar auren a matsayin halattacce ba.
Matan Zeher su biyu; Dilber da Ikramiye Gezer sun ce suna murna da tsarin iyalansu, duk da yake kowace ta haifi ’ya’ya maza da mata kuma suna ba da gudunmawarsu ga sauran iyalan.
Uwargidan Zeher, Dilber wadda ta haifi ’ya’ya 10, ta ce, “Da farko na nuna kishi kan karin auren da Zeher ya yi, amma daga bisani muka kasance kamar ’yan uwan juna.
“Tana da ’ya’ya ni ma ina da su don ’ya’yan kishiyata, ’ya’yana ne, ’ya’yana ’ya’yanta ne.”
Zeher ya ce, yana fata zai iya ciyar da iyalansa da kansa, amma ya rasa aikinsa saboda bullar annobar Coronavirus.
Zeher ya ce, “Da a ce na san haka zata faru, da ban haifi ’ya’ya da yawa ba.”
’Ya’yan Zeher 19 suna kwana ba tare da sun ci abinci ba inda suke fatan hukumomi su kawo masu agaji.