Mahaifina ne Bahaushen da ya fara auren Ba-yarabiya a Legas -Inji Hawwa mai shekara 82
Wata dattijuwa mai shekara 82 da aka haifa a birnin Ikko da ke Jihar Legas, mai suna Hauwa Abubakar ta ce mahaifinta shi ne Bahaushen da ya fara auren Bayarabiya a jihar ta Legas.Hajiya Hauwa, wacce mahaifinta xan asalin garin Haxeja ne da iyayensa suka zauna a garin Gwaram, ta yi furucin hakan ne yayin […]

Wata dattijuwa mai shekara 82 da aka haifa a birnin Ikko da ke Jihar Legas, mai suna Hauwa Abubakar ta ce mahaifinta shi ne Bahaushen da ya fara auren Bayarabiya a jihar ta Legas.
Hajiya Hauwa, wacce mahaifinta xan asalin garin Haxeja ne da iyayensa suka zauna a garin Gwaram, ta yi furucin hakan ne yayin wata tattaunawa da Aminiya a kwanakin baya, inda ta bayyana mahaifinta Abubakar da ake yi wa laqabi da Baban Nuhu ya zo Legas tun bai yi auren fari ba.
Ta ce, “Ni a unguwar Itafaji aka haife ni, a titin Liman da ke cikin birnin Ikko. Mahaifina yana xaya daga cikin Hausawan da suka zo Legas, shekaru da dama da suka wuce. Shi ne Bahaushe na farko da ya auri Bayarabiya mai suna Saratu a jihar ta Legas. Saboda a lokacin babu Hausawa da yawa a Legas. Kana iya qididdige yawansu, ba kamar yanzu ba da mutanenmu suka yi yawa. A da kowa ya san kowa”.
Ta ci gaba da nuna asalin da take da shi a jihar, inda take da takardar haihuwarta ta jihar. “Na taso a lungun Dadi da ke tsakiyar birnin Ikko. Mahifina xan Jonhol ne. Mun zauna da Yarabawa, zaman aminci da amana. Ba za ka tava jin an yin faxa tsakanin Bayarabe da Bahaushe ba. Don a lokacin akwai gaskiya da riqon amana”. Inji ta.
Ta bayyana cewa Hausawa sun je Legas tun kafin zuwan Turawa, ba tare da wata matsala ba. “Tun a wannan lokacin Hausawa ne suke da abin duniya don a wurinsu Yarabawa kan ci abinci. A lokacin ba sa qyamar mu ba sa kuma qin cin abincin da muka ba su. Mun zauna da jinsin Yarabawa iri-iri, kamar Yarabawan Oyo da ake kira Aroake; da Yarabawan Isenyi da Yarabawan garin Offa lafiya. Su ne suke xebo mana ruwa, su ne suke yi mana aikin abinci da sauran ayyukan gida. A lokacin akwai unguwar matsafa a can wajen birnin Ikko, ba sa shigowa cikin gari, sai idan za su yi tsafinsu, sai su zo su sanar da Hausawa cewa kada su fito waje, za su yi tsafinsu na gargajiya kuma har su gama bikin tsafin, ba za ka ji an yi tashin hankali ba”.
Hajiya Hauwa, wacce take mamakin yadda Hausawa da Yarabawa suke rikicin qabilanci a tsakaninsu, ta ce a lokacinsu a Kudu da Arewa ba haka lamarin yake ba.
Hausawa da dama da Aminiya ta tuntuva waxanda suka haxa da Alhaji Muntari Alin Magaji da Manjo Daba, mai ritaya da Hajiya Asabe da aka haifa a Legas, sun tattabar da iqirarin da Hajiya Hauwa ta yi.