Mahaifina ne kaɗai shugaban da bai damu ya azurta kansa ba — Seyi Tinubu

Shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa.

Mahaifina ne kaɗai shugaban da bai damu ya azurta kansa ba — Seyi Tinubu

Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, mahaifinsa ne kaɗai shugaban ƙasar da ba shi da burin azurta kansa da kuɗin talakawa.

Har wa yau ya ƙara da cewa shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa.

Seyi ya faɗi hakan ne yayin yi wa wani dandazon matasa jawabi a Yola, babban birnin Jihad Adamawa.

Seyi Tinubu wanda ke ci gaba da shawagi a wasu jihohin ƙasar yana buɗa-baki, ya ce a kwanakin wasu sun dage wajen sukar mahaifinsa, sai dai hakan ba zai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen kawo ci gaba a Nijeriya.

Har wa yau, Seyi ya ce mahaifinsa ne kaɗai ne shugaban da ya samar da yanayin tattalin arziki da kowa ke amfana a ƙasar a halin yanzu.

“Shi kaɗai ne shugaban ƙasar da ba shi wata manufa ko burin azurta kansa.”

A bayan nan ne tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya zargi Gwamnatin Tinubu da rashawa.

Cikin sabon littafin da ya ƙaddamar yayin bikin cikarsa shekaru 88, Obasanjo ya caccaki Gwamnatin Tinubu kan abin da ya kira ɓarna da almubazzaranci musamman dangane da yadda ta kashe kimanin Naira biliyan 21 wajen gina wa Mataimakin Shugaban Kasa katafaren gida.