Mahaifina ne ya sanya ni fashi da makami-Bode Oladejo

daya daga cikin ’yan fashin da rundunar ’yan sandan jihar Legas ta kama a karshen makon da ya gabata mai suna Bode Oladejo ya ce  mahaifinsa ne ya jefa shi cikin fashin da makami.Bode Oladejo dan kimanin shekaru 22 a duniya dan asalin garin Oro da ke jihar Kwara , saboda halin ko-in-kula da mahaifinsya […]

Mahaifina ne ya sanya ni fashi da makami-Bode Oladejo
Mahaifina ne ya sanya ni fashi da makami-Bode Oladejo

daya daga cikin ’yan fashin da rundunar ’yan sandan jihar Legas ta kama a karshen makon da ya gabata mai suna Bode Oladejo ya ce  mahaifinsa ne ya jefa shi cikin fashin da makami.
Bode Oladejo dan kimanin shekaru 22 a duniya dan asalin garin Oro da ke jihar Kwara , saboda halin ko-in-kula da mahaifinsya nuna wajen daukar dawainiyarsu ne ta tilasta masa yin sace-sace har daga bisani ya fada fashi da makami.
Ya ce ‘Tun ina shekaru 11 nake karya kofofin jama’a ina yi musu sata. Kuma rashin kula da mu da mahaifinmu ba ya yi a gida shi ya sa na shiga sata don na dauki nauyin kaina. Akwai lokacin muna Ikorodu mai gidan da muke haya ya kore mu daga gidan saboda mahaifina ya kasa biyan haya. Mahaifina sam bai damu ba, a maimakon haka ma sai ya yi tafiyarsa garin Ibadan. Ita kuwa mahaifiyata sai ta ci gaba da zama a Ikorodu. Daga nan sai na zama dan gareji, ni nake ciyar da kaina’.
Ya ci gaba da cewa ‘Tun shekarar 2003 nake fashi da makami saboda yadda mahaifinmu ya yi watsi da mu. Na fara da yin amfani da adda har na sami bindiga daga wurin wani abokina mai suna Monday, wadda na saya Naira dubu 30; nakan yi fashi a yankin Iyana Oba da unguwar Okokomaiko. Daga bisani sai wani abokina ya gayyace ni unguwar Ajegunle don mu yi fashi, inda na kan samu kimanin dubu 50 a fashi. Daga bisani ’yan sanda suka kama mu’.
daya daga cikin ’yan fashin da aka kama su tare mai suna Opene daga jihar Delta, ya ce ya gayyaci abokansa ne su yi wa wani makwabcinsa fashi saboda laifin da ya yi masa.
Shi ma dan fashi na uku mai suna Nwachie dan shekaru 20 a duniya, ya ce ya fara sata ne tun yana shekara 16 da haihuwa, kuma ya yi wa fasinjoji da yawa fashi.
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta bayyana cewa a lokacin da ta samu cikakken bayani game da ’yan fashin sai ta ummarci rundunar yaki da fashi da makami karkashin jagorancin Abba Kyari su kamo su.
Ta ce cikin sa’a sai suka samu nasarar kama su, amma daya daga cikin ’yan fashin ya gudu ana nemansa ruwa a jallo.
Rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike a kansu za ta gurfanar da su a kotu.