Mahaifinmu uba ne na kwarai – Mansur kasimu Yero
Mansur kasimu Yero shi ne babban dan marigayi Alhaji kasimu Yero fitaccen dan wasan kwaikwayo da fina-finan Hausan nan da ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana wa Aminiya cewa hakika sun yi babban rashi domin mahaifinsu ya ba su gudunmawa sosai wajen inganta rayuwarsu musamman wajen ganin sun samu ilimi. Ga […]

Mansur kasimu Yero shi ne babban dan marigayi Alhaji kasimu Yero fitaccen dan wasan kwaikwayo da fina-finan Hausan nan da ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana wa Aminiya cewa hakika sun yi babban rashi domin mahaifinsu ya ba su gudunmawa sosai wajen inganta rayuwarsu musamman wajen ganin sun samu ilimi. Ga yadda hirar ta kasance:
Mene ne sunanka da dangartakarka da marigayi kasimu Yero?
Sunana Mansur kasimu Yero ni ne dan marigayi Alhaji kasimu Yero na farko kuma shekaruna 45. Marigayin ya bar ’ya’ya takwas, maza uku mata biyar kuma ya rasu yana da shekeru 70 a duniya. Ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya. Kuma Allah Ya yi masa cikawa ne a ranar 3 ga Satumba wadda ta yi daidai da 12 ga watan Zul-Hajjin bana.
Wato ya yi fama da rashin lafiya ke nan?
Gaskiya ya yi fama da rashin lafiya sosai kafin Allah Ya yi masa rasuwa.
Mata nawa ya bari?
Gaskiya bai bar mace ba, domin matarsa ta riga shi rasuwa.
Me za ka iya tunawa game da mahaifinku?
Abin da zan iya tunawa shi ne ba kamar yadda mutane suke kallonsa a talabijin ba, cewa mutum ne mai yawan wasa da dariya. Wannan fuska ce tashi ta talabijin amma a zahiri mutum ne mai tarbiya kuma ba ya son ganin an yi ba daidai ba. Mutum ne da ke son ganin duk abin da mutum zai aikata, to ya yi shi da kyau. Yana kuma son ganin mutane na zuwa makaranta ko su kama sana’a domin dogaro da kai. Amma ba yadda mutane ke ganinsa yana yawan ban dariya da sauransu ba, su dauka ko a zahiri haka yake.
Ko akwai wani abu da idan ka tuna game da shi yana saka alfahari da kasancewarsa mahaifinku?
Eh, gaskiya abin da zan iya tunawa shi ne babu kamar gudunmawar da ya ba mu a matsayin ’ya’yansa ta wajen neman ilimi da tabbatar da cewa mun yi karatun, sannan mun dan samu abin da za mu rika yi a rayuwa. Wannan abu na daya daga cikin abubuwan da na fi tunawa da shi. Sai kuma mukan samu alfarma ta dalilinsa.
Ke nan akwai alfarma da kuke samu a wasu lokuta ta dalilinsa?
Eh, kwarai kuwa domin idan muka fita wani lokaci idan jama’a suka tambaya aka ce ai ’ya’yan wane ne sai ka ga ana jawo mu a jiki tare da karrama mu da yi mana abin da muke so. Da wuya ka ga mun je waje an ce ’ya’yan wane ne ba ka ga wani na kokarin jawo mu a jiki ba ko neman taimaka mana. Ko idan wani abu muke nema za ka ga ana son yi mana. Ka ga wannan abu ne da ba za mu iya mantawa ba sannan abu ne da za mu rika tunawa da shi duk da cewa a yau babu shi. Ka san sha’anin rayuwa ba mu san yadda zai kasance ba amma tabbas ina tabbatar maka da haka muke samu a sha’anin rayuwarmu duk inda muka je za ka ji mutane na cewa ga ’ya’yan wane ga ’ya’yan wane, wadansu ma har zuwa suke suna kallonmu kamar wasu abubuwa na daban. Haka rayuwarmu ta kasance.
Ko a cikin ku ’ya’yansa akwai wanda ya shiga wasan kwaikwayo?
Eh, kwarai kuwa akwai kanena Aminu wanda shi ke bi na shi ma ya shiga fannin Baba din yana yi, sai dai da yake yana yi yana karatu ne bai yi nisa ba, domin ba a san shi sosai ba kamar mahaifinmu. Amma yana bin layinsa domin ya dauko layinsa kuma wadansu sun san shi, saboda haka a cikinmu dai shi ne kawai ya dauko wannan layi.
Ko akwai wani abu da za ka so jama’a su rika tunawa da da shi game da mahaifinku?
Abin da nake son jama’a su rika tunawa, shi ne kamar fannin fadakarwa da nishadantar da jama’a da kuma gwada wa jama’a al’adunmu da wayar da kan mutane da sanin ya kamata da yin abin da ya kamata da kuma barin abin da bai kamata ba. Wannan abu nake so idan mutane suka duba suka ga irin wasanninsa da ya yi a baya ko a talibijin ko rediyo za ka ga cewa yana yin su ne domin wayar da kan al’umma da ilimantar da su domin su fahimci abubuwan da suka kamata su rika yi da kuma wadannda ba su kamata ba.
Ban sani ba ko ku ’ya’yansa kuna kallon wasu daga cikin wasanninsa?
Eh, muna kallo wasu lokuta duk da yake ka san wasannin a yanzu kusan sun bace saboda wasannin zamani da suka zo, amma dai idan muka samu muna kallo duk da cewa wasu wassannin na tsofaffin wasanni ne. Wadansu daga cikin kannena ma da yawa wasu wasannin lokacin da aka yi su ba a haife su ba. Kamar ni dai na san wasu da yawa na kuma kalli wasu da yawa.
Ko ya taba fada maka tarihi da yawan wasannin da ya yi a lokacin rayuwarsa?
Ya sha ba ni tarihi amma gaskiya ko shi kansa ban yi tsammanin zai iya fada maka yawan wasannin da ya yi ba balle ni. Koda yana da rai sai dai ya kiyasta maka amma dai na san ya taba fada min sannan kuma an taba yin hira da shi a wata kafar watsa labarai da yake cewa ya san ya rubuta wasanni kusan dubu biyu a rayuwarsa. Rubutawa kawai ba shiryawa ba. Amma iya wasannin da ya yi ba zan iya cewa nawa ne ba.
Yaya batun karramawa da lambobin yabo?
Wadannan kam ya samu da yawan gaske ba su da iyaka shi kansa bai san yawansu ba. Amma wadanda suka fi girma a lambobin yabo da ya samu biyu ne na farko shi ne wanda ya samu ina ji a1989 lokacin mulkin Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida aka ba shi MFR na biyu kuma lokacin mulkin Shugaban kasa Obasanjo a shekarar 2001 na san an kara ba shi MON. Wadannan ne dai manyan lambobin yabo na kasa da na san an ba shi ban da kananan lambobin yabo da aka yi ta ba shi wadanda ban san yawansu ba.
Me za ka ce ga dimbin masoyansa dangane da wannan rashi da aka yi?
Abin da zan ce da su shi ne babu kamar su yi masa addu’a domin addu’a ya fi bukata a yanzu . Sannan su yi koyi da kyawawan halayensa da ya koyar a baya. Yanzu abin da kawai zan ce masu ke nan tunda ya riga ya tafi wani waje wanda mu ma muna kan hanya.