Mahaifiyar Babban Editan jaridar Daily Trust ta rasu

A safiyar Litinin ne Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan, Hajiya Rabi (Umma) cikawa a Jihar Kano

Mahaifiyar Babban Editan jaridar Daily Trust ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan Jaridar Daily Trust, Hamza Idris rasuwa.

Kaninsa, mai suna Aminu Idris, ya bayyana cewa a safiyar Litinin ne Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan, Hajiya Rabi (Umma) cikawa bayan gajeruwar jinya a Jihar Kano.

Za a gudanar da jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya ranar a Layin Ɗorawar ’Yan Kifi da ke unguwar, Rijiyar Zaki, Kano.

Daga nan za a kai ya maƙabartar Walid Mai Zage da ke Kofar Mazugal.

Muna roƙon Allah Ya yi mata rahama, Ya ba wa dangi haƙurin rashin da kuma dangana.