Mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma ta rasu
Babu tabbacin ko tsohon gwamnan zai halarci jana’izar mahaifiyar tasa.
Nasir El-Rufai
Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ta riga mu gidan gaskiya.
Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne, ya sanar da rasuwar kakar tasa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.
- Najeriya ta doke Iran da ci 2 a wasan sada zumunta
- Abduljabbar ya nemi taimakon alƙalin alƙalai kan zargin yi wa shari’arsa maƙarƙashiya
“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Daga Allah muka fito kuma gare Shi za mu koma. Ina sanar da jama’a rasuwar kakata, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta riga mu gidan gaskiya sa’o’i kaɗan da suka gabata,” in ji shi.
Bello, ya gode wa Allah kan tsawon rayuwar da ta yi mai cike da albarka. Y
a kuma roƙi Allah Ya jiƙan ta da rahama, tare da neman al’umma su nema mata rahamar Ubangiji.
Ya ƙara da cewa: “Mun gode wa Allah kan rayuwar da ta yi, muna roƙon Allah Ya jiƙan ta da rahama… A madadin iyalinmu, muna neman addu’o’inku.”
Wannan rashi ya zo ne a daidai lokacin da El-Rufai ke fuskantar shari’a, biyo bayan kama shi da aka yi tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan wasu zarge-zarge.
Wannan yanayi ya janyo shakku da tattaunawa kan ko tsohon gwamnan zai samu damar halartar jana’izar mahaifiyar tasa.