Mahaifiyar Farfesa Ibrahim Malumfashi ta rasu

Za a yi jana’izarta bayan sallar Juma’a a Unguwar Dosa da ke Kaduna.

Mahaifiyar Farfesa Ibrahim Malumfashi ta rasu

Farfesa Ibrahim Malumfashi

Allah Ya yi wa mahaifiyar fitaccen farfesan adabin Hausa, Ibrahim Malumfashi rasuwa.

Farfesan ne da kansa ya sanar da rasuwar mahaifiyar tasa a daren nan na Alhamis.

Ya ce, “Inna lilLaHi Wa Inna ilaihil raji’un! Yanzu Allah Ya karbi ran mahaifiyata, Fatima.”

Za a yi jana’izarta bayan sallar Jumu’a da misalin karfe 1:30 a masallacin Sheikh Mahmoud Jafar da ke Unguwar Dosa, kusa da gidajen ‘yan Majalisa a Jihar Kaduna.