Mahaifiyar Farfesa Umaru Pate ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Kashere, Farfesa Umaru Pate rasuwa.

Mahaifiyar Farfesa Umaru Pate ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Kashere, Farfesa Umaru Pate rasuwa.

Farfesa Umaru Pate mashahurin malamin aikin jarida ne kuma ya koyar a jami’o’i da dama, kama daga Jami’ar Maiduguri, Jami’ar Bayero, da Jami’ar Jihar Kaduna da dai sauransu.

Mahaifiyarsa tasa, Diddi Hussaina ta rasu ne tana shekara 70.

Ta kwanta dama ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama, baya fama da rashin lafiya.

Farfesa Umaru Pate ya tabbatar da rasuwar yana mai cewa an gudanar da jana’izar mahaifiyar tasa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.