Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Za a yi jana’izarta da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Laraba.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, Hajiya Maryam Namadi, rasuwa.

Ta rasu da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Disamba, 2024.

Labarin rasuwar, na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, za a yi jana’izarta da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a garin Kafin Hausa.

Gwamnan, da iyalansa sun buƙaci ɗaukacin Musulmi da su yi mata addu’ar samun rahama daga Allah.