Mahaifiyar Ministan Ƙwadago ta rasu
An yi jana’izar mahaifiyar Ministan Ƙwadago wadda ta rasu tan da shekara 93.
![Mahaifiyar Ministan Ƙwadago ta rasu Mahaifiyar Ministan Ƙwadago ta rasu](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/01/20250103_105222.jpg)
Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa Abubakar, mahaifiyar Ministan Kwadagon Nijeriya, Muhammmad Maigari Dingyaɗi, rasuwa.
Hajiya Hauwa Abubakar ta rasu ne a ranar Alhamis tana da shekara 93, bayan ta yi jinya na tsawon lokaci.
An yi mata jana’iza a ranar Juma’a da safe gidan Ministan da ke unguwar Polo a birnin Sakkwato.
Gwamna Sakkwato Ahmad Aliyi, a sakon ta’aziyyarsa, ya bayyana kaduwarsa da rashin mahaifiyar ministan.
“Rasuwar Hajiya Hauwa’u rashi ne da ke taba zuciya tabbas mun yi rashi uwa abin son mu,’” in ji gwamnan, a cikin saƙon.
Hajiya Hauwa’u ta rasu tana da shekarru 93 ta bar ‘ya’ya biyu da jikoki da dama.