Mahaifiyar Pele ta rasu

Tun tana da shekara 17 Celestinha ta haifi Pele a watan Oktoba na shekarar 1940.

Mahaifiyar Pele ta rasu

Pele tare da mahaifiyarsa Celeste Arantes

Mahaifiyar fitattacen ɗan kwallon kafa na duniya wato Pele ta riga mu gidan gaskiya a Brazil, watanni 18 bayan tasa rasuwar.

Celeste Arantes wadda ta koma ga Mahaliccinta a ranar Juma’a ta rasu bayan shafe shekaru 101 a doron ƙasa.

Tun tana budurwa ’yar shekara 17 Arantes ta haifi ɗanta na fari wato Pele a ranar 23 ga watan Oktoba na 1940, wanda ya zamo tauraro a duniyar kwallon kafa da wasu ke ikirarin ba a yi kamarsa ba.

Babban ɗan marigayi Pele, Edinho ne ya bayyana rasuwar kakarsa cikin wani saƙon hoto da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Kawo yanzu dai babu wani bayani dangane da musabbabin mutuwarta, sai dai kafofin watsa labarai na cikin gida sun bayyana cewa tun kwanaki takwas da suka gabata a kwantar da Arantes a Asibiti.

Pele tare da mahaifiyarsa Celeste Arantes

Ana iya tuna cewa, danginta sun yi ikirarin cewa ba ta da masaniya kan mutuwar ɗanta saboda Arantes tana fama da ’yan matsaloli na zautuwa da tsofaffi tukuf suka saba fuskanta.

Celeste Arantes dai ta auri mahaifin Pele, Joao Ramos do Nascimento tun tana ’yar shekara 16, kuma sun haifi wani ɗan mai suna Jair da ya rasu sanadiyyar cutar daji a shekarar 2020 — cutar da ita ce ta yi ajalin Pele.

Cikin wani saƙon taya murnar zagoyowar ranar haihuwa a lokaci da ta cika shekara 100, Pele wanda ya saba kiranta da Celestinha ya wallafa wasu hotuna uku a shafinsa na Instagram da ke nuna lokuta daban-daban na rayuwarsu.

Bayan kwanaki tara da wallafa saƙon ne a kwantar da Pele a wani Asibitin a birnin Sao Paulo, inda a nan wa’adinsa a duniya ya cika.

Pele wanda asalin sunansa na yanka shi ne Edson Arantes do Nascimento, shi kaɗai ne ɗan kwallon ƙafar da a tarihi ya lashe Gasar Kofin Duniya sau uku da suka haɗa da ta shekarar 1958 da 1962 da 1970.

 

AFP

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda