Mahaifiyar Rarara: Masu garkuwa na neman N1bn
Sun bukaci tattaunawa kai-tsaye da Rarara wanda tun da aka sace mahaifiyarsa yake fama da rashin lafiya
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara sun bukaci a biya kudin fansar ta Naira biliyan daya.
Majiyar Aminiya a kauyen Kahutu, inda aka yi garkuwa da Hajiya Hauwa’u Adamu, ya bayyana cewa masu garkuwar sun kira iyalan ta waya suna neman kudin tare da shaida musu cewa babu abin da ya same ta.
Majiyar, wadda ke da kusanci da iyalan dattituwar, ta ce ’yan bindigar “sun kira ne ta wayar wata ’yar gidan a lokacin da suka kai harin da suka sace Hajiya.
“Sun nemi a biya kudin fansa Naira biliyan daya, amma bayan tattaunawa da wani dan gidan suka rage kudin zuwa miliyan N900.
“Da farko sun nemi tattaunawa ne da Rarara, amma kasancewar ba shi da lafiya tun bayan da suka sace ta, sai suka amince su yi magana da wani dan gidan.
“Sun tabbatar wa iyalan cewa Hajiya na cikin koshin lafiya kuma za su sake ta da zarar an biya kudin.
“ Cikin dan kankanin lokaci suka yi tattaunawar kuma har yanzu ba su sake kira ba.
“Amma duk hakan ina da yakikin ana ci gaba da tattaunawa da su.
“Iyalan na jiran ’yan bindigar su sake kira, a ci gaba da tattaunawa,” in ji majiyar, wadda ke da kusanci da gidansu Rarara.
Yadda aka sace mahaifiyar Rarara
Dangane da yadda aka sace mahaifiyar mawakin kuwa, majiyar ta ce bisa dukkan alamu ’yan bindigar sun tsara abin sosai.
A cewarta, da hoton dattijuwar suka zo suna neman ta domin kar su yi kuskure wajen daukar ta.
“Mun samu labari cewa har uwar dakin Hajiya suka shiga suka tayar da duk matan da ke barci tare da ita, suka rika bin su guda-guda suna duba hoton domin gane wadda suke neman.
“Da suka gano ta, sai suka nemi ta ba su kudi, sai ta nuna musu kuɗin da ke cikin durowar gefen gadonta, amma suka ga kudin babu yawa.
“A karshe sai suka umarce ta da ta biyo su, ita kuma ba tare da bata lokaci ba ta bi umarnin nasu.”
Majiyar ta ci gaba da cewa garkuwa da Hajiya Hauwa’u ya girgiza al’ummar kauyen Kahutu.
A cewar majiyar, dattijuwar na da karimci, kuma ta zama uwa ga iyalai da dama.
“Hajiya ta dauki nauyin hidimar aurar da ’ya’yan marasa karfi da marayu da dama a kauyen Kahutu da wasu makwabtanmu.
“Kusan babu wanda zai ce bai amfana da alherin Hajiya ba a yankin nan, domin babu wanda zai kai mata kuka, ya dawo ba tare da ta share masa hawaye ba.
“Kowa shaida ne a kan hakan,” in ji majiyar.