Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu

Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta.

Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu

Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya.

Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya.

Haka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta.

Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza.

A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a Ƙaramar Hukumar Gwoza.

Rasuwar Hajiya Asta Shehu Timta dai wani babban rashi ne ga masarautar ta Gwoza bisa ga irin gudummawar da ta ke bayarwa ga al’umma.