Mahaifiyar Sarkin Ilori mai shekara 124 ta rasu
Allah Ya yi wa mahaifiyar Mai martaba Sarkin Ilori na jihar Kwara Alhaji Ibrahim Sulu Gambari rasuwa, a daren Sallah karama wato a jajibirin ranar sallah Hajiya Aisha Zulkannaini Gambari ta rasu tana da shekaru 124 a duniya inda aka yi jana’izar ta a ranar Sallah a fadar sarkin Ilori bayan an saukko daga Sallar Idi karama. […]
Allah Ya yi wa mahaifiyar Mai martaba Sarkin Ilori na jihar Kwara Alhaji Ibrahim Sulu Gambari rasuwa, a daren Sallah karama wato a jajibirin ranar sallah
Hajiya Aisha Zulkannaini Gambari ta rasu tana da shekaru 124 a duniya inda aka yi jana’izar ta a ranar Sallah a fadar sarkin Ilori bayan an saukko daga Sallar Idi karama.
Marigayiyar jika ce ga Sarkin Ilori na 7, ‘ya ga Sarkin Ilori na 8 sannan mata ga sarkin Ilori na 9, ‘Yar uwa ga Sarkin Ilori na 10 kana uwa ga Sarkin Ilorin na 11.
Muna fatan Allah ya jikanta tare da magabatan mu baki daya.