Mahaifiyar tsohon shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar shugaban Hukumar yaki da almundahana (EFCC) Abdulrasheed Bawa rasuwa.

Mahaifiyar tsohon shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ta rasu

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban Hukumar yaki da almundahana (EFCC) Abdulrasheed Bawa rasuwa.

Mahaifiyar Abdulrasheed mai suna Hajiya Hadiza Ahmed Bawa ta rasu ne a garin Sakkwato ranar Laraba da dare.

Abdulrasheed Bawa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa “Ta rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodio, amma za a yi jana’izarta ne a Jega, Jihar Kebbi, inshaAllah da misalin 2:30.”

Aminiya ta gano cewa ana kan shirye-shiryen kai gawar dattijuwar zuwa jihar Kebbi domin janai’zar a ranar Alhamis.

Abdulrasheed Bawa shi ne farar hula na farko da ya zama shugaban EFCC mai cikakken iko, a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2021, daga bisani majalisar dokoki ta kasa ta amince da naɗin nasa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

A watan Yuli 2023 kuma, bayan hawa mukin Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7