Mahaifiyar tsohon shugaban kasa Yar’Adua ta rasu

Za a yi jana’izar Hajiya Dada ranar Talata bayan Sallar Azahar a Katsina

Mahaifiyar tsohon shugaban kasa Yar’Adua ta rasu

Allah Ya yi wa Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adua rasuwa.

Iyalan Yar’Adua sun sanar cewa Hajiya Dada ta rasu ne a daren Litinin da misalin karfe 7 na dare, tana da shekaru 102.

Sun kuma bayyana cewa za a yi jana’izar dattijuwar da misalin karfe 1.30 na ranar Talata a gidansu da ke Katsina.

Hajiya Dada ta rasu ya bar ’ya’ya da jikoki, ciki har da Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdulazeez Musa Yar’adua.

Hajiya Dada ita ce Allah Ya yi wa albarka da ’ya’yan da suka taɓa zama shugaban ƙasa, mataimakin shugaban kasa, gwamna, sanata, a lokcin rayuwarta.

Kuma ta binne biyu daga cikinsu, ɗaya yana kan kujerar shugaban kasa.