Mahajjata miliyan 1.7 sun kammala tsayuwar Arfah
An samu ƙarin adadin mahajjata idan aka kwatanta da bara, inda aka samu mahajjata 1,673,230.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa jimillar mahajjata 1,707,301 ne suka gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2026.
Alƙaluman da hukumar ta fitar bayan kammala tsayuwar Arfah yayin aikin Hajjin na shekarar 1447 bayan hijira sun nuna ƙarin adadin mahajjata idan aka kwatanta da bara, inda aka samu mahajjata 1,673,230.
- Bikin Sallah: Zulum ya ayyana dokar taƙaita zirga-zirga ta wucin-gadi a Borno
- Atiku ya lashe zaɓen fidda gwanin ADC a Kano
Hukumar ta ce ƙididdigar ta ƙunshi dukkan mahajjata maza da mata da suka halarci aikin Hajjin a Makkah da sauran wurare masu tsarki.
A yammacin wannan Talatar ce dai mahajjatan suka kammala tsayuwar Arfah, inda za su kwana a Muzdalifah sannan washegari su koma Mina a matsayin wasu manyan rukunai na farillan Hajji.
Mahukuntan Saudiyya sun ce sun yi tanadin matakan tsaro, lafiya da jigilar jama’a domin tabbatar da walwala da sauƙin gudanar da ibadu ga mahajjata.
Hajji na daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, kuma wajibi ne a kan duk musulmin da Allah Ya hore wa hali da lafiya ya sauke shi sau ɗaya a rayuwarsa.