‘Mahajjatan da suka rasu a Saudiyya sun haura dubu 2’
Adadin mahajjatan da suka rasu a turmutsitsin da ya faru a Muna lokacin aikin hajjin bana ya rubanya wanda hukumomin kasar Saudiyya suka bayar tun farko, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya bayyana a farkon makon nan. A ranar Litinin da ta gabata ne aka ruwaito cewa akalla mahajjata 2,110 ne suka rasu […]
Adadin mahajjatan da suka rasu a turmutsitsin da ya faru a Muna lokacin aikin hajjin bana ya rubanya wanda hukumomin kasar Saudiyya suka bayar tun farko, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya bayyana a farkon makon nan.
A ranar Litinin da ta gabata ne aka ruwaito cewa akalla mahajjata 2,110 ne suka rasu sakamakon turmutsitsin da ya faru a ranar 24 ga watan jiya lokacin jifan shedan.Wadannan alkaluman an same su ne daga kafafen yada labarai da kuma kasashe fiye da 30 wadanda suka mahajjatansu.
Tun bayan faruwar al’amarin, hukumomin kasa-Mai-Tsarki ba su kara cewa uffan ba, bayan wata sanarwa da aka fitar washegarin ranar, inda da aka ce mahajjata 769 ne suka rasu. Aka kuma bayyana wasu guda 934 da suka samu raunuka.
Sai dai kasar Iran tana ikirarin cewa ta rasa mahajjatan kimanin 465, wannan ya sa ta zama kasar da ta fi kowace asarar jama’arta sakamakon hadarin. Kodayake, kasashen nahiyar Afirka su ma sun rasa mahajjata da dama misali: Najeriya ta rasa guda 199, sai kasar Mali mai mahajjata 198 da kuma kasar Masar mai 192, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Rahoton yana zuwa ne kwana guda bayan hukumomin Saudiyya sun yi wani taro kan lamarin. Kuma an bayyana cewa ana ci gaba da binciken abin da ya faru a Muna lokacin jifan shedan, kamar yadda Sarki Salman ya ba da umarni.
Hadarin ya kasance ma fi muni a cikin kimanin shekaru 25. Turmutsitsi ma fi muni bayan na bana shi ne wanda ya faru lokacin aikin hajjin shekarar 1990, inda mahajjata 1,426 suka rasa rasukansu.