Mahajjatan Kaduna dubu 1,084 suka tashi zuwa Saudiyya- Hukuma

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa, a yanzu haka mahajjatan jihar Kaduna dubu 1,084 suka isa kasar Saudiyya don gudanar hajjin bana 2019. Kakakin Hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a yau Litinin. Jirgin mahajjatan Kaduna na biyu ya tashi ne da mahajjata 545 daga […]

Mahajjatan Kaduna dubu 1,084 suka tashi zuwa Saudiyya- Hukuma

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa, a yanzu haka mahajjatan jihar Kaduna dubu 1,084 suka isa kasar Saudiyya don gudanar hajjin bana 2019. Kakakin Hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a yau Litinin.

Jirgin mahajjatan Kaduna na biyu ya tashi ne da mahajjata 545 daga babban filin jirgin sama na Kaduna da misalin karfe 5:05 na safiyar yau yayin da mahajjatan farko na jihar suka tashi ranar Asabar.

Akwai adadin mahajjata maza 683 da mata 404 da suka tafi a jirgin saman Med View.