Mahama zai sake yin takarar shugabancin Ghana
A ranar Asabar da ta gabata ne jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) mai mulki a kasar Ghana ta gudanar da zaben fidda gwani don tsayar da wanda zai yi mata takarar shugabancin kasa da kuma na kujerun majalisar dokokin kasar.Kodayake, Shugaba John Dramani Mahama ba shi da abokin hamayya a zaben, kuri’an da a kayi […]
A ranar Asabar da ta gabata ne jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) mai mulki a kasar Ghana ta gudanar da zaben fidda gwani don tsayar da wanda zai yi mata takarar shugabancin kasa da kuma na kujerun majalisar dokokin kasar.
Kodayake, Shugaba John Dramani Mahama ba shi da abokin hamayya a zaben, kuri’an da a kayi ne mambobi za su amsa Eh ko A’a, wato wadanda ke son shugaban ya tsaya wa jam’iyyar, su amsa Eh, wadanda ba su amince ya ci gaba ba, su amsa A’a.
A karshen zaben dai kashi 95 cikin 100 na wadanda suka yi zaben sun amince shugaban ya tsaya wa jam’iyyar takara a babban zaben badi. Yayin da kashi hudu suka jefa kuri’ar kin amincewa da takararsa. Kashi guda kuma kuri’unsu sun lalace.
A lokacin da Shugaba Mahama yake jawabi bayan samun nasararsa ya ce, “A matsayina na shugaba na san cewa ba kowa ne ya gamsu da abubuwan da na yi a shekaru uku ba. Amma duk da haka na ji dadin amincewar da na samu daga jam’iyyar NDC, kuma na sha alwashin jagorantar jam’iyyar domin mu samu nasara a zaben badi.”