Mahangata: Makomar gundumar Bakori da danja a babban zaben bana

A wannan makon, mun samu tsokaci ne daga Khabir Sa’idu Khaleel (08062576909), wanda ya zayyana mahangarsa a siyasance, dangane da al’amuran zaben wakilai a gundumarsa ta Bakori da danja. Shi me yake cewa ne? A wannan karon zan so in yi amfani da damar da na samu, domin in yi wani tsokaci a kan gundumar […]

Mahangata: Makomar gundumar Bakori da danja a babban zaben bana
Mahangata: Makomar gundumar Bakori da danja a babban zaben bana

A wannan makon, mun samu tsokaci ne daga Khabir Sa’idu Khaleel (08062576909), wanda ya zayyana mahangarsa a siyasance, dangane da al’amuran zaben wakilai a gundumarsa ta Bakori da danja. Shi me yake cewa ne?

A wannan karon zan so in yi amfani da damar da na samu, domin in yi wani tsokaci a kan gundumar Bakori da danja, dangane da zabubbukan da ke tafe a wannan lokaci.
Zan dauki jam’iyya da mutumin da ke takara a karkashinta daya-bayan-daya.
Bari mu fara da jam’iyya mai mulkin gundumar a yanzu, wato jam’iyyar APC. Jam’iyya ce wadda jama’a suka bayyana a matsayin mai adalci da sanin ya kamata da kwato hakkin talakawa da ganin babu kamarta a fadin jam’iyyun kasar nan. A haka ne ma suke ganin cewa sai dai su yi bakin-rai-bakin-fama wajen tsare akwatinan zaben da jaddada ganin an ba wanda suka zaba.
Amma kash, a wannan gundumar ba haka ba ne, don kuwa ta canza zani; ta yadda muka daddage a zaben 2011 muka yi wa jam’iyyar CPC ruwar kuri’u, ashe zaben tamun dare muka yi, domin zuwa yanzu ba wani aiki da wani dan majalisar da zai nuna ya ce shi ya yi shi. Hasali ma idan ya zo kamfen, sai dai ya ce a yi APC sak, a madadin ya nuna ayyukan da ya yi, kafin ya ci gaba da kamfen da su. To mu yanzu ba ruwanmu da sak, cancanta za mu bi, domin kuwa ba wani ci gaba a bangaren ilmi da ya kawo, ba wani dalibi guda daya da ya dauki nauyinsa a bangaren karatu koda kuwa tallafin fom din JAMB ga dalibai ko littattafai ga makaratun firamari ko sakandare.
A bangaren kasuwanci kuwa, ba a cewa komai domin kuwa mun gwammace ma a ce Bakori da danja ba mu da wakili a Abuja, ina ganin hakan zai fi mana kwanciyar hankali. Kai, wallahi wannan ya ci amanar jam’iyyar APC da talakawa. Wai ina Naira miliyan 130 din da ake ba ka don ka yi wa gundumarmu aiki? Me ka yi wa ’yan bangar siyasar da suka yi ma wahala a shekarar 2011? Koma dai mene ne, za mu gani a akwatin zaben 28 03 2015.
Jam’iyyar PDP, jam’iyya ce wadda ta kai makura wajen takura wa talakawa, wajen cuta da zalunci da danniyar zabe da hana su duk wata walwala da jin dadi a kasar nan. Don haka ne ma talakawa ke ganin cewa babu wani adalci a jam’iyyar ko wani dan jam’iyyar. Don haka suke da kudirin runtuma ta da kasa a babban zabe mai zuwa.
Amma kash, mu a gundumarmu ba nan gizo ke sakar ba. Domin kuwa jam’iyyar ta a je mutum wanda bai yi kama da ’yan jam’iyyar ba, domin kuwa mutum ne mai ra’ayin Turawa. Don haka ne ma talakawa ke tsoron kada su yi mai ruwan kuri’u, a zo kuma a koma ’yar gidan jiya. Domin kuwa mutum ne attajiri amma kuma ba ya taimakon kowa. Me ya sa ba zai yi taimako da aljihunsa ba, sai ya hau mukamin majalisar wakilai? A wani bangaren kuma jama’a suna zarginsa da share shekara da shekaru bai zo mahaifarsa ba, a lokacin da yake aiki a Abuja. Don haka suke ganin koda sun yi masa laftun kuru’u ya tafi, ba zai dawo ba kamar yadda ya saba. Sai dai kuwa ba a nan take ba, sai an gwada akan san nakwarai.
A mahangata shi ne, wannan al’amari na gundumata shi ne gaba kura baya sayaki. Shin za mu bar zaben ne kwata-kwata? Domin kuwa duk wanda ya ce biri dan kwarai ne, to ya kai shi gonarsa. Makomar dai ba ta wuce ’yar gidan jiya ba. Ma’ana, an gudu ba a tsira ba.
Allah Ka zaba mana mafi alheri.