Mahara sun ƙone Sakatariyar Karamar Hukuma bayan janyewar ’yan sanda
Ƙasa da awa biyar da janye ’yan sanda, mahara sun ƙona Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Eleme a Jihar Ribas.
Ƙasa da awa biyar da janye ’yan sanda, mahara sun ƙona Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Eleme a Jihar Ribas.
Kafin wayewar gari ne Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, ya umarci jami’ansa sun janye daga sakatariyar ƙananan hukumomi 23 da ke jihar.
Wani mazaunin garin Eleme ya shaida wa wakilinmu cewa, ya ce ɓata-gari ɗauke da muggan makamai ne suka far wa sakatariyar ƙaramar hukumar, suka Banks mata wuta.
“’Yan davan sun farfasa tagogin ginin da ba su kama da wuta ba.
“Sun kai harin ne awanni kaɗan bayan shugaban ’yan sanda ya umarci jami’ansa su janye daga sakatariyar ƙananan hukumomin,” in ji shi.
Wakikinmu bai samu jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Ribadu, SP Grace Iringe-Koko, zuwa lokacin haɗa wannan labari ba.