Mahara sun farmaki ɗan takarar gwamna, sun sace matarsa a Benuwe
Maharan sun buƙaci Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.
’Yan bindiga sun kai wa ɗan takarar gwamnan jami’yyar APC a zaɓen 2023, a Jihar Benuwe, Mista Terwase Orbunde, hari tare da yin awon gaba da matarsa.
Orbunde, ya tsira da harbin bindiga a hannunsa na dama a yayin harin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Sewuese Anene, ta shaidabwa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), cewa ’yan bindigar sun kai wa Orbunde da iyalansa hari ne lokacin da suke dawowa daga gona.
Ta ce Orbunde ya kai rahoton harin ga ’yan sanda, inda aka aike tawaga zuwa wajen da lamarin ya faru.
Anene, ta ce rundunar na bin sahun maharan domin kubutar da matarsa ɗan takarar da suka sace.
Shaidu sun ce Orbunde da matarsa da kuma ’yar aikinsu sun je zagayen gona ne lokacin da lamarin ya faru.
Bayan sun sallami ma’aikatansu ne, wasu ’yan bindiga biyar suka farmake su tare da yin awon gaba da wasu zuwa daji.
Harbin bindigar da maharan suka yi ne, ya sa mutanen kauyen da ke kusa da masu wucewa suka yi ta kansu.
Wata majiya ta shaida wa NAN cewa maharan sun buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 100 kafin sako matan biyu da suka sace.