Mahara sun harbe basarake har lahira a Ogun

Maharan sun shiga gidan suka harbe shi har lahira amma ba su dauki komai ba.

Mahara sun harbe basarake har lahira a Ogun

Wasu ’yan sandan Najeriya a bakin aiki

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta tabbatar da kisan wani basarake a masarautar Shagamu a Jihar Ogun, Cif Bashorun Abiodun, yayin da wasu mahara suka harbe shi har lahira.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru a daren ranar Litinin.

“Lamarin ya faru da misalin karfe 8 na daren ranar Litinin, yayin da wasu mutum uku dauke da bindigu suka shiga gidan Cif Bashorun Abiodun a garin Shagamu, suka harbe shi har lahira ba tare da daukar komai a gidan ba.

“Ranar Talata aka yi jana’izar marigayin mai rike da sarautar Baasegun ta Itunsokun, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” in ji majiyar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abiodun Alamutu, wanda ya jagoranci rundunar zuwa gidan marigayin, ya ce “Mun fara daukar matakin binciken bankado masu hannu a kisa.

“Za mu tabbatar sun shiga hannu domin girbar abin da suka aikata,” in ji Kwamishinan ‘yan sandan.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu