Mahara sun kashe basarake, sun sace mutum 10 a Taraba
Jami’an tsaro sun mamaye yankin domin dakile ayyukan ’yan bindiga da masu satar mutane.
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka Sarkin Garin Moddibo da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola a Jihar Taraba.
Sarkin mai suna Alhani Muhammadu ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ’yan bindigar suka shiga garin kuma suka kai hari har fadarsa.
- ’Yan ta’adda sun kashe wani babban limami a Borno
- Kotu ta daure ’yan daudun da suka yi shigar mata da rawa a Kano
Bayanai sun ce maharan sun kuma sace matar basaraken da dansa daya da kuma karin wasu mutane hudu a garin.
Kazalika, ’yan bindigar sun sace mutane hudu ciki har da wata matar aure mai shayarwa a wasu kauyuka da ke kusa da garin na Moddibo.
Wata majiya ta alakanta kisan da ’yan bindigar suka yi wa sarkin kan goyon bayan da yake yi wa ’yan banka da suke gadin garin domin hana ’yan bindigar rawar gaban hantsi.
Shugaban Karamar Hukumar Ardo-Kola, Dalhatu Kawu, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari da cewar tuni an kai wa gwamnatin Jihar Taraba rahotan abin da ya faru.
Dalhatu Kawu ya bayyana cewa ’yan sanda masu yaki da ’yan ta’adda suna yankin tare kungiyar mafarauta domin dakile ayyukan ’yan bindiga da masu satar mutane wadanda suka addabi yankin.
Shi ma kakakin rundunar ’yan sanda Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai bai bayar karin bayani ba.