Mahara sun kashe manoma 6 a kauyen Malumfashi
A cewar mazauna yankin, ’yan bindigar sun riga sun yi barazanar kashe duk wani manomi da aka gani a gona a wannan kakar noman.
Akalla mutane shida sun mutu a wani hari da ’yan ta’adda suka kai kauyen Gidan Gaje da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina.
A Maharan sun kai wa kauyen manoman harin ne a safiyar Alhamis, a bisa babura inda suka mamaye kauyen, suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin ya tilasta mata da yara guduwa cikin dazuka domin tsira. A ranar da abin ya faru aka yi jana’izar mutanen bisa tsarin addinin Musulunci.
Shaidu sun ce masu maharan da suka kai harin a kauyen Gidan Gaje—da ke mazabar Layin Minista/Tashar Fulani/Marabar Kankara—yaran wani sanannen shugaban ’yan bindiga da ya addabi yankin Kankara–Malumfashi ne, mai suna Babaro.
Al’ummar yankin sun ce tun da farko ’yan bindigar sun riga sun yi barazanar kashe duk wani manomi da aka gani a gona a wannan kakar noman.
- An kama kwamandojin Boko Haram 7 a Katsina bayan sun dawo aikin Hajji
- An kori kamfanin Gombawa Motors daga tashar gwamnati bayan goyon bayan Pantami
“Sun gargade mu cewa duk wanda ya je gona za a kashe shi. Da yawa sun daina noma saboda tsoro. Amma waɗanda suka yi watsi da gargadin su ne aka kai wa hari,” in ji wani mazaunin yankin.
Wani jagoran al’umma, wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce ’yan bindigar na yawo cikin kauyuka ba tare da tsoron gwamnati ba, suna sa ido kan manoma sannan daga baya su kai hare-hare.
“Suna shigowa kauyukanmu tamkar babu gwamnati. Sukan zo a fili su yi barazana, daga baya kuma su dawo su kai hari. Mutane sun zama ba su da kariya,” in ji shi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa tun farkon kakar noman bana, wadda ta ƙara ƙarfi a ’yan makonnin da suka gabata, ’yan ta’adda sun kashe sama da mutane 20 a hare-haren daban daban kaman al’ummomin manoma a yankin.
Mazauna yankin sun ce yawan hare-haren sun tilasta daruruwan mutane barin gidajensu da gonakinsu, abin da ke haifar da barazanar ƙarancin abinci.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro ko gwamnatin Jihar Katsina kan lamarin. Ƙoƙarin jin ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Ƙasa, Nasiru Mu’azu Danmusa, bai yi nasara ba, domin ba a amsa kira da saƙonnin da aka tura masa ba.