Mahara sun kashe matashi, sun dauke mahaifiyarsa a Jigawa
Ana fargabar wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Sabo Yusuf a yankin Kawo na Jihar Jigawa. Zahraddeen Aminuddeen wanda ke zaman Kakakin rundunar ’yan sandan jihar shi ne ya inganta rahoton kamar yadda manema labarai na BBC suka ruwaito. PDP za ta yi watsi da tsarin karba-karba a 2023 Ba sace ni […]
‘Yan Sanda
Ana fargabar wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Sabo Yusuf a yankin Kawo na Jihar Jigawa.
Zahraddeen Aminuddeen wanda ke zaman Kakakin rundunar ’yan sandan jihar shi ne ya inganta rahoton kamar yadda manema labarai na BBC suka ruwaito.
- PDP za ta yi watsi da tsarin karba-karba a 2023
- Ba sace ni aka yi ba, guduwa na yi – Amaryar Kano
- ’Yan bindiga: Sheikh Gumi yana mana katsalandan – Masari
A cewarsa, maharan sun kai hari gidansu Sabo da tsakar daren Laraba, inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da kuma wani dan uwansa.
Kakakin ya ce Sabo ya rasu ne a wani Asibitin Birnin Kudu da aka garzaya da shi bayan maharan sun harbe shi a kirji.
“Da misalin karfe 3:35 na daren Laraba ne ’yan sandan Birnin Kudu suka samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun far wa gidan Alhaji Abubakar mai shekara 50 a Kawo.”
“Sun harbi dansa a kirji mai suna Sabo Yusuf dan shekara 25,” a cewar Kakakin.
Ya kara da cewa, a halin yanzu dai Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tura jami’ai rundunar yaki da maki zuwa yankin.