Mahara sun kashe mutane 40 a Filato

Wadanda aka kashe sun hada da ’yan banga a kauyen Zurak da ke Gundumar Bashar a Karamar Hukumar Wase.

Mahara sun kashe mutane 40 a Filato

Rahotanni daga Jihar Filato na nuni da cewa mahara sun kashe mutane sama da 40 a Karamar Hukumar Wase.

Wadanda maharan suka kashe sun hada da ’yan banga a harin na kauyen Zurak da ke Gundumar Bashar a karamar hukumar.

Wani shugaban matasan yankin mai suna Sahpi’i Sambo, ya ce maharan sun kai farmakin ne a bisa babura dauke da muggam makamai suna har kan mai uwa da wabi.

A cewarsa, “Sama da mutum 40 aka kashe wasu da dama kuma sun samu raunuka.  Sakamakon haka, al’ummar kauyen sun yi kaura, zuwa wasu wurare.

“Zuwa jiya (Litinin) dai jami’an tsaro ba su iso yankin ba, amma harin ya yi muni kwarai,” in ji  Sambo.

Mazauna yankin sun cewa a yammacin ranar Lahadi ne maharan suka kai farmakin a yayin da jama’a ke tsaka da garkokinsu na yau da kullum.

Wani mazaunin garin mai suna rashin karfin layin sadarwa ya hana su sanar da jaim’an tsaro domin kawo musu dauki.

Zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton, kakakin ’yan sanda jihar, DSP Alabo Alfred, bai samu amsa bukatarmu ta karin haske game da harin ba.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa