Mahara sun kashe mutane 5 a masallaci a Nasarawa

mutanen da aka kashe a masallacin sun yi gudun hijira ne daga wasu kauyuka da ’yan bindiga addaba

Mahara sun kashe mutane 5 a masallaci a Nasarawa

An kashe mutane biyar a cikin masallaci a wani hari da ’yan bindiga suka kai a kauyen Katakpa da ke Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.

Wakilinmu ya gano cewa mutane biyar din da aka kashe sun samu mafaka a masallacin da ake Katakpa ne bayan sun yi gudun hijira daga wasu kauyuka da ’yan bindiga addaba.

Wani mazaunin kauyen , mai suna Ibrahim Yakubu, ya shaida mana cewa da misalin karfe 2 na dare ne ’yan bindiga suka yi wannan aika-aika a masallacin.

Ya bayyana cewa karan harbe-harben ’yan bindigar ya sojoji garzayawa domin kawo wa al’ummar kauyen dauki.

Ya ci gaba da cewa sojojin sun yi musayar wuta da ’yan bindigar kuma sun yi nasarar kashe da dama daga cikinsu.

Yakubu Ya bayan cewa an gano cewa ’yan bindigar sun ajiye baburansu ne suka tako zuwa kauyen a cikin dare kafin wayewar garin ranar Alhamis.

Wakilinmu ya gano cewa mutane biyar din da aka kashe a masallacin ’yan gudun hijira ne da suka samu mafaka kauyen.

Shugaban Karamar Hukumar Toto,  Alhaji Abdullahi Aliyu Tashas, ya tabbatar da harin.

Daga ranar 14 ga watan Fabrairun 2024 zuwa yanzu, ’yan bindiga sun kai hare-hare da dama kauyen na Katakpa inda suka kashe mai unguwar yankin da kuma sojoji da dama.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe