Mahara sun kashe mutane 6 a kasuwa a Filato

Mahara sun kashe mutane shida a kasuwar yankin Congo a Karamar Hukumar Bokkos.

Mahara sun kashe mutane 6 a kasuwa a Filato

Mahara

Rahotanni daga jihar Filato na cewa mahara sun kashe mutane shida a kasuwa a yankin Bokkos.

Shaidu sun ce akalla mutum daya ne aka jikkata a harin da aka kai unguwar Congo da ke karamar hukumar.

Majiyoyi a yankin sun ce an kai wanda aka jikkata a harin zuwa asibiti ana ba shi kulawa.

Sun bayyana cewa da misalin karfe 7 na dare ne maharan suka kai farmaki a kasuwar yankin, suna harbi kan ma uwa da wani.

Harin da aka kai jim kadan bayan yawancin ’yan kasuwa sun tashi, ya jefa mazauna cikin zullumi.

Wakilinmu ya nemi samun karin bayani daga kakakin ’yan sanda na jihar Filato, DSP Alabo Alfred , amma jami’in bai amsa kiransa ba.