Mahara sun kashe mutane goma a Adamawa ’Yar kunar bakin wake ta kashe takwas a Yobe

Wasu mahara da ake zargin ’yan Boko Haram sun kashe mutum goma a sabon harin da suka kai a wata unguwa da ke Ajiya Wagga a karamar Hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa. Wannan harin ya zo ne bayan wani hari da suka kai a ranar Juma’ar makon jiya a Unguwar Sabon Gari a karamar […]

Mahara sun kashe mutane goma a Adamawa ’Yar kunar bakin wake ta kashe takwas a Yobe
Mahara sun kashe mutane goma a Adamawa ’Yar kunar bakin wake ta kashe takwas a Yobe

Wasu mahara da ake zargin ’yan Boko Haram sun kashe mutum goma a sabon harin da suka kai a wata unguwa da ke Ajiya Wagga a karamar Hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa. Wannan harin ya zo ne bayan wani hari da suka kai a ranar Juma’ar makon jiya a Unguwar Sabon Gari a karamar hukumar inda mutum daya ya rasu kuma aka kwantar da mutum shida a asibiti.

Mista Warga Sunday wanda ya tsira daga harin a Unguwar Ajiya Wagga ya ce ’yan bindigar sun shiga unguwarsu ne da tsakiyar dare bayan kowa ya kwanta barci suka fara harbe-harbe a inda suka kashe wasu a unguwar.
“Na ga gawarwaki da dama a kwance a lokacin da nake kokarin tsira da raina. Mutane da yawa har yanzu na cikin daji domin tsoron haduwarsu da ’yan bindigar wasu kuma sun gudu zuwa kauyukan da ke kusa,” inji shi.
Wani da ya tsira, mai suna Mista Luka Murkus ya ce mutane da dama sun samu rauni sosai kuma an kai su asibiti domin yi musu jinya.
Ya ce, “Sun shigo mana ne da tsakiyar dare a ranar Asabar sannan suka kashe mutum goma.”
Shugaban karamar hukumar, Maina Ularamu ya yi kira ga gwamnati ta kara tsaro a wuraren da abin ya auku.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Adamawa, DSP Othman Muhammed ya ce ’yan sanda na jiran rahoto kan harin.
Daga Jihar Yobe kuwa, wata ’yar kunar bakin wake ne ta kai hari a bayan tashar motar Damaturu, wanda ya yi sanadin hallaka mutum takwas tare da jikkata mutum 37 da galibinsu kananan yara ne.
Malam Saleh Bakwaro da ke cikin tashar motar lokacin da lamarin ya faru ya shaida wa Aminiya ce ’yar kunar bakin waken ta kai harin ne da misalin karfe 11:00 na safe.
Malam Saleh ya ce ’yar kunar bakin waken da shekarunta ba su wuce 12 ba, ta yi kokarin shiga tashar ne amma kokarin gano abin da ke jikinta da masu bincikar masu shiga tashar ta karamar kofa ne ya sa ta tada bam din da ke jikinta, inda ta yi kaca-kaca
wasu bama-bamai uku da ke jikinta kuma ba su fashe ba.
Ya ce ya ga gawarwaki akalla mutum shida da kuma mutum 37 da suka jikkata da jami’an tsaro suka kwashi su zuwa asibiti.
Jim kadan da faruwar lamari ne Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya kai ziyara asibitin Damaturu don duba mutanen da harin ya rutsa da su, inda Gwamnan ya bayyana harin da na rashin imani da Allah zai azabtar da duk wanda ke da hannu a ciki.
Gwamnan ya nemi jama’a su ci gaba da sa ido kan duk wani ko wata da ba su gane take-takensu ba, don kama su tare da mika su ga jami’an tsaro.
Ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin jinyar dukkan wadanda suka ji rauni tare da bada umarnin wadanda a kai wadanda rauninsu ya yi muni cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya da ke garuruwan Azare da Nguru da asibitin Malam Aminu Kano don yi musu jinya.
Babban Likitan Asibitin Tunawa da Marigayi Sani Abacha da ke Damaturu Dokta Garba Musa Fika ya tabbatar da mutuwar mutum bakwai nan take, sai mutum 37 da suka jikkata yayin da bakwai daga cikinsu raunukansu suka yi tsananin da za a tura su manyan asibitoci.