Mahara sun kashe mutum 11 a Binuwai

Hare-haren sun salwantar da rayukan mutum 11 tare da raunata wasu.

Mahara sun kashe mutum 11 a Binuwai

’Yan bindiga

Akalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da mahara suka kai Karamar Hukumar Agatu ta Jihar Binuwai.

Wannan na zuwa ne mako guda da harin da wasu ’yan bindiga suka kai yankin Odugbeho a Karamar Hukumar tare da kashe mutum 27.

  1. ’Yan sanda sun dakile harin ’yan fashi a Kaduna
  2. Mutumin da ya fi kowa yawan iyalai a duniya ya kwanta dama

Wakilinmu ya rawaito cewar maharan sun kashe mutum biyu a yankin Odugbeho, sai mutum tara a kauyukan Aila da Adagbo

Shugaban Karamar Hukumar ta Agatu, Adoyi Sule, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewar ana zargin wasu makiyaya ne suka kai harin.

Ya kuma ce mutum takwas sun samu raunuka, kuma tuni aka garzaya da su asibiti don ba su kulawa ta musamman.

Sai dai da wakilinnmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, DSP Catherine Anene, ta ce ba ta da masaniya kan faruwar harin.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa