Mahara sun kashe mutum 18 a Gwoza, 15 sun halaka a Wukari
Rahotanni daga garin Gwoza da ke Jihar Borno sun ce wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutum 18 a safiyar ranar Talatar da ta gabata ciki har da dagacin garin.Wani mutum da ya kubuta daga harin ya bayyana cewa maharan na sanye da kayan sojoji ne.Kuma bayanai sun […]
Rahotanni daga garin Gwoza da ke Jihar Borno sun ce wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutum 18 a safiyar ranar Talatar da ta gabata ciki har da dagacin garin.
Wani mutum da ya kubuta daga harin ya bayyana cewa maharan na sanye da kayan sojoji ne.
Kuma bayanai sun nuna cewa ana samun karuwar kai hare-hare a Jihar Borno duk da cewa jihar tana karkashin dokar ta-baci.
A cikin makon jiya ma an kashe fiye da mutum 100 a garuruwa daban-daban na Jihar Borno.
Kuma a ranar Talata da daddare ’yan bindiga sun kai hari garin Wukari da bke jihar Taraba, inda suka jefa jama’ar bgarin cikin zaman zullumi.
Bayanai sun cewa kimanin mutum takwas sun rasa rayukansu a harin da aka kai a wani kauye da ake kira Nwunkyo-Kura a kusa da garin Wukari.
Kuma mutum bakwai sun rasa rayukansu a wani lamari mai kama da martani ga harin da aka kai tun farko a kauyen.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Joseph Kwaji ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce tuni aka tura jami’an tsaro domin maido da doka da oda a garin.