Mahara sun kashe mutum 18, sun sace magidanci da ’ya’yansa a Benuwe
Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike a yankin.
’Yan bindiga sun kai hari unguwar Mbache da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala a Jihar Benuwe, inda suka kashe mutum 18 tare da sace wani mutum da ’ya’yansa biyu.
Shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar, Mista Justin Shaku ne, ya tabbatar da faruwar lamarin.
- Yadda mai sayar da kifi ya saci zinare, ya sayar da shi 60m
- Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano — SEMA
Ya ce sun samun kiran neman agaji da misalin ƙarfe 11:00 na dare kan cewar mahara sun kai hari yankin.
Shaku, ya bayyana cewar maharan sun tattara mutanen waje ɗaya ne kafin daga bisani suka harbe su a lokaci ɗaya.
Shi da sauran jami’an yankin sun gana tare da sanar da kwamishinan ‘yan sanda faruwar lamarin.
A cewarsa, harin ya tayar da hankulan mazauna yankin kan yiwuwar dawowar ayyukan ƙasurguman ‘yan bindiga.
Ya bayyana fatan cewa yanayin tsaro zai inganta, duk da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu.
Shugaban ya bayyana cewar duk da taɓarɓarewar sha’anin tsaro da aka fuskanta a yankin a baya, amma an samu zaman lafiya kafin sake aukuwar wannan harin.
Ya buƙaci al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu tare da ba su tabbacin cewa Gwamna Hyacinth Alia ya himmatu wajen magance matsalolin tsaro a jihar baki ɗaya.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Sewuese Anene, ya tabbatar da kai harin kuma ya bayyana cewa ana gudanar da bincike a kai.
Anene, ya tabbatar wa jama’a cewa an ƙara yawan jami’an tsaro a yankin kuma ya buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu.
A cewarsa jami’an tsaro na aikin don daƙile duk wata barazanar tsaro a Katsina-Ala.