Mahara sun kashe mutum 42 a Borno ..Sun kashe sojoji 18 da ’yan sanda 15 a Yobe
Rahotanni daga garin Gurmushi da ke karamar Hukumar Marte a Jihar Borno sun ce an kashe akalla mutum 42 a wani hari da ’yan bindiga suka kai a safiyar shekaranjiya Laraba.’Yan bindigar wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne bayan kashe mutanen, sun kuma raunata wasu dama tare da kona daukacin gidajen garin.Wata mata da […]

Rahotanni daga garin Gurmushi da ke karamar Hukumar Marte a Jihar Borno sun ce an kashe akalla mutum 42 a wani hari da ’yan bindiga suka kai a safiyar shekaranjiya Laraba.
’Yan bindigar wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne bayan kashe mutanen, sun kuma raunata wasu dama tare da kona daukacin gidajen garin.
Wata mata da ta tsira daga harin ta shaida wa gidan rediyon BBC a harshen Kanuri cewa “Ina daga cikin wadanda suka tsira, an kona garin baki daya. Na ga gawarwaki 42.”
An garzaya da wasu daga cikin mutanen da suka samu raunuka zuwa wani gari da ke kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.
Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a kan kauyukan jihohin Borno da Yobe.
A Jihar Yobe ’yan bindigar da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun hallaka sojoji 18 da ’yan sanda 15 a wani mummunan hari da suka kai ga mazaunin jami’an tsaro na JTF da ke garin Buni Yadi a karamar Hukumar Gujba.
Wata majiya a Buni Yadi ta shaida wa Aminiya cewa, ’yan bindigar sun je garin ne da misalin karfe 5:00 na yamma a ranar Litinin, cikin motocin HILUd dauke da fentin sojoji da wata motar yaki ta soja inda jami’an tsaron da ke gadin kofar shiga masaukin suka dauka ’yan uwansu ne sai suka bude musu kofa, bayan ’yan bindigar sun shiga sai suka fara bude wuta ba kakkautawa.
Wani mazaunin Buni Yadi da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya ce, bayan ’yan bindigar sun gama aika-aikarsu a gidajen jami’an tsaron sai suka far wa babban ofishin ’yan sandan karamar hukuma suka kone, sannan suka shiga gari suka kone gidan Hakimi Alhaji Abba Hassan Mai Mukhtar da Babbar Kotun Majistare da ofishin Hukumar INEC da kananan motoci hudu.
Ya kara da cewa lokacin da ’yan bindigar suka shiga garin sun rika fada wa mutane cewa ba su zo domin su ba don haka ne ba za su taba kowa ba.
Wani da ya samu nasarar tserewa daga garin na Yadin Buni ya shaida wa Aminiya a Damaturu cewa ya kirga gawarwakin jami’an tsaro akalla 30 ban da wadanda suka ji raunuka.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin kakakin JTF a jihar Kyaftin Eli Lazarus ya ci tura, a yayin da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar aka ce suna ganawa da Mataimakin Gwamnan Jihar Injiniya Abubakar Ali da sauran shugabannin tsaro.