Mahara sun kashe mutum 9 a Benuwe
Mahara sun kai farmaki wasu ƙauyuka uku na Jihar Benuwe.
Akalla mutane tara ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hare-haren da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai wasu ƙauyuka na Jihar Benuwe.
Mazauna sun ce lamarin ya faru ne a ranakun Juma’a da Alhamis a wasu ƙauyukan kananan hukumomin Apa da Agatu.
- Magidanta uku na taƙaddama kan mallakar ’ya’yan wata mata a Oyo
- Zan tsaya takarar shugaban Chadi — Mahamat Deby
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “A ranar 1 ga Maris, 2024, maharan sun kashe wani mutum ɗaya a ƙauyen Edikwu Icho bayan harin da suka kai a Ikobi.
Haka kuma, a wannan rana, sun kashe mutane biyu a ƙauyen Akpanta na Karamar Hukumar Apa, tare da kashe mutum ɗaya a ƙauyen Ugbobi, shi ma a Karamar Hukumar Apa, inda aka kashe jimillar mutane huɗu.”
Barista Eche Akpoko, wanda shi ne shugaban kungiyar ci gaban Apa, ya ce adadin waɗanda suka mutu na iya karuwa saboda har yanzu akwai waɗanda aka nema aka rasa.
Akpoko a wannan Asabar ya shaida wa wakilinmu a birnin Makurdi cewa, an kai hare-haren ne lokaci guda da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, sai dai ya jaddada cewa har yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da aka kashe har sai an kammala bincikensu.
Hakazalika, wani basaraken gargajiya a Agatu, Cif James Edoh, ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyar a yankinsa a wani hari da aka kai ƙauyen Alokpa da misalin karfe 5 na yamma. ranar Alhamis.
Ya ce, ba tare da bata lokaci ba aka kai rahoto ga dukkan hukumomin tsaro da ke aiki a yankin, ciki har da ‘yan sanda.
Shi ma dan majalisa mai wakiltar mazabar Agatu a majalisar dokokin jihar, Godwin Edoh, ya tabbatar da kashe mutanen biyar, inda ya ce harin ya faru sau biyu a Alokpa a ranakun Laraba da Alhamis.
Edoh ya ce, “An kai hare-hare tsakanin ranar 28 zuwa 29 ga watan Fabrairu a Alokpa inda aka kashe mutane biyar.
“Akwai wani hari da aka kai a Obagaji inda mata da yara suka ranta a na kare bayan da suka ji ƙarar harbe-harbe daga Alokpa, wani kauye da ke makwabtaka da shi, amma ba a kai wa Obagaji hari ba.”
Wakilinmu ya ƙoƙarin jin ta bakin jami’ar hulɗa da jama’a ta ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, sai dai an yi rashin sa’a ba ta amsa kiran wayarta ba.