Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa
Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun harbe mutum tara har lahira tare da jikkata wasu da dama a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun harbe mutum tara har lahira tare da jikkata wasu da dama a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
Da misalin ƙarfe 8 na dare ne maharan suka kai farmaki suna harbi kan mai uwa da wabi a yankin Tattara ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “bagatatan suka far mana a cikin dare, mutum tara sun rasu wasu biyu na kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai baya ga wasu da suka raunuka da dama.”
Kimanin shekara guda ke nan da aka kai makamancin harin tare da ƙona gidaje a yankin na Tattara.
Wakilinmu ya lura ’yan sanda na ƙoƙarin daidaita al’amura a yankin a ranar Lahadi, sai dai ƙoƙarinsa na yin magana da kakakin rundunar na jihar Nasarawa bai yi nasara ba, kuma wayar jami’in ba ta shiga.