Mahara sun kashe mutum sun sace 17 ’yan gida daya

’Yan bindiga sun harbi mutum uku ’yan gida daya suka kuma yi garkuwa da 17

Mahara sun kashe mutum sun sace 17 ’yan gida daya

Yadda ‘yan bindiga ke ta’annatinsu a dazukan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Mutumin da masu garkuwa da mutane suka harba a lokacin da suka yi dauke iyalansa a Jihar Kaduna ya rasu.

’Yan bindiga sun tare Omega da ’yan uwansa a hanyarsu da zuwa gona inda suka yi awon gaba da mutum 17 daga cikinsu a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

“Ya rasu da misalign 3.00 na asuba a Birnin-Gwari inda ake jinyar sa, kafin muka dawo da shi Udawa muka binne shi da misalin 10 na safe”, inji kawunsa, Malam Umaru.

Wakilimun ya jiyo cewa baya ga mamacin wanda ’yan bindigar suka harba a baki, mata biyu ’yan uwansa da su ma suka samu munanan raunuka a harin suna kwance a asibiti a Birnin-Gwari.

Ya ce dole ta sa aka mayar da marasa lafiyar asibitin daga inda aka fara kai su a Kaduna saboda iyalan ba za su iya biyan kudin asibiti ba.

Har yanzu babu labarin ’yan uwan su 17 da aka yi garkuwa da su, wadanda a cikinsu har da mace mai shayarwa da jaririnta.

Kafin hada wannan rahoto, wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jagile, amma bai amsa kiran wayasan ba kuma babu wata sanarwa daga Rundunar game da harin da aka kai wa iyalan.