Mahara sun kashe ’yan sanda bakwai a Jigawa

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kashe jami’anta bakwai a wani hari da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai a garin Gwaram da ke jihar a ranar Talatar da ta gabata cikin dare. Mataimakin Sufeto Janar mai kula da shiyyar Kano, Alhaji Muhammadu Tambari Yabo ya shaida wa manema labarai a […]

Mahara sun kashe ’yan sanda bakwai a Jigawa

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kashe jami’anta bakwai a wani hari da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai a garin Gwaram da ke jihar a ranar Talatar da ta gabata cikin dare.
Mataimakin Sufeto Janar mai kula da shiyyar Kano, Alhaji Muhammadu Tambari Yabo ya shaida wa manema labarai a Dutse cewa maharan da yawansu ya kai 200 a kan babura da motoci da ake zargin ’yan fashi ne ko mahara suka kai harin, inda suka hallaka ’yan sandan kwantar da tarzoma hudu da ’yan sanda uku da kuma wani maigadin bankin Unity da ke garin na Gwaram.
Alhaji Tambari Yabo ya ce tun misalin karfe 1:00 na dare maharan suka fara barin wuta har karfe 4 na asubar shekaranjiya Laraba.
Ya kara da cewa, zuwa lokacin da yake wa manema labarai bayani, ba su samu labarin ko maharan sun dauki kudi a bankin ko ba su dauka ba, kuma idan sun dauka ba su san adadin kudin ba.
Ya ce bayan kura ta lafa ne jami’an ’yan sanda da safiyar shekaranjiya Laraba suka ga inda aka yi gumurzu da maharan ya yi faca-faca da jini, amma ba su samu ko da gawar mutum daya na maharan ba.
Ya ce maharan sun yi amfani da bama-bamai da miyagun makamai wajen kai harin.
Alhaji Tambari ya ce kamar suna da masaniya a kan za a kai harin, domin sun jibge ’yan sandan masu yawa a yankin kuma hakan ne ya sa maharan ba su cim ma burinsu ba.
Ya ce maharan da suke dauke da makamai masu yawa sun zo wurin ne a kan wadansu manyan babura da motoci har ma daya daga cikin motarsu, wadda ake zaton daga Jihar Bauchi suka sato ta suka bar ta a nan saboda ta samu matsala, suka sake satar wata mota a karamar hukumar ta Gwaram suka yi gaba da ita.
Shi ma dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Alhaji Yusif Shitu Galambi ya ce lamarin ba kyan gani, domin ya ga gawarwakin da ’yan sanda suka yi wa manema labarai bayani, ya kuma jajanta wa jama’ar yankin. Ya ce ba wannan ne karo na farko ba, an taba samun irin wannan harin a cikin shekarar da ta gabata har ta kai ga halaka rayuka da kone bankin na Unity da ke karamar Hukumar Gwaram.