Mahara sun kone gida tare da kashe mutum 3 a Toro

Wadansu mahara da ake zargin barayi ne, sun kai hari gidan Shugaban kungiyar mafarauta ta Danga Security da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Yusuf Abdullahi, da ke garin Magama, inda suka bude wuta da bindigogi suka kashe masu gadin gidan uku, tare da kone gidan baki daya cikin dare ranar Asabar da […]

Mahara sun kone gida tare da kashe mutum 3 a Toro
Mahara sun kone gida tare da kashe mutum 3 a Toro

Wadansu mahara da ake zargin barayi ne, sun kai hari gidan Shugaban kungiyar mafarauta ta Danga Security da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Yusuf Abdullahi, da ke garin Magama, inda suka bude wuta da bindigogi suka kashe masu gadin gidan uku, tare da kone gidan baki daya cikin dare ranar Asabar da ta gabata.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan lamarin, shugaban kungiyar mafarautan ta Danga Security, wanda kuma mai harkokin kasuwancin sayar da ma’adinai ne, ya ce bayan ya fita gida yana garin Magama Gumau a ranar da lamarin ya faru, bayan Sallar Magriba, sai ya taso zai taho gida Magama, sai makwabcinsa ya kira shi a waya ya ce masa barayi sun shigo gidansa, har sun sanya wa gidan wuta.

Ya ce nan take ya kira jami’an tsaro na Magama Gumau ya fada musu, ya kira mai Gundumar garin ya fada masa. “Yayana ya je wajen da aka ajiye sojoji a kusa da garin Magama ya fada musu abin da ke faruwa, suka ce ba a ba su umarni ba. Hankalina ya tashi, na tashi zan tafi wajen ’yan sanda suka hana ni, saboda babu wani makami a hannuna. Wadannan ’yan ta’adda sun sanya wuta a gidan kuma matana 2 da ’ya’yana 9 duk suna ciki,” inji shi.

Ya ce bayan da mabarnatan suka tafi da suka zo suka tarar sun kone gidan baki daya kuma sun kashe masu gadi  uku da suka hada da Umar Fareti da Auwalu Muhammad da kuma Jamilu.

Ya ce kafin wadannan miyagu su kone gidan, sun shiga ciki suka yi ta harbe-harbe da bindigogi amma Allah Ya tserar da iyalansa babu wanda ya rasa ransa.

Ya ce mayagun sun shaida wa amaryarsa cewa ta gaya masa cewa sata yanzu suka fara kuma wai ya bar aikin nan da yake yi, idan ya bar aikin nan ya rabu da su, shi ke nan. Idan kuma bai bar aiki nan ba, yana nan tare da su; domin a cewarsu, wai ya takura musu.

Shugaban ya ce ganin yanayin abubuwan da suke faruwa a karamar hukumar, na yadda barayi suke damunsu da ta’addanci da fashi da makami ya sa ya shiga wannan aiki. 

“Babu shakka na takura wa barayi a yankin Toro ta hanyar wannan kungiya da nake yi wa jagoranci ta Danga Security, domin na sha kama barayi da bindigogi ina kai wa jami’an tsaro amma su dawo. Wadansu ma ba su fin mako biyu, sai a sako su. Wadannan mutane suna ta fadin cewa za su kashe ni, na sha rubuta korafi ina kai wa jami’an tsaro kan wannan lamari. Ina rokon a daina sako irin wadannan mutane da nake kamawa,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti kan faruwar lamarin, ya tabbatar da cewa lamari ya faru. Ya ce sun je gidan mutumin tare da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi, don ganin abin da ya faru. Ya ce  suna ganin kamar maharan sun zo ne don su hallaka mutumin, domin ba su dauki komai ba a gidan. Amma sun kashe masu gadin gidan mutum uku, kuma sun kone gidan baki daya. Ya ce suna nan suna bincike don gano mutanen da suka aikata wannan mugun aiki don gurfanar da su a gaban kotu.