Mahara sun sace basarake da matarsa a Kogi

Daga Tijani Labaran, Lokoja Mahara sun sace wani basarake, Oba na Idofin da matarsa a hanyar Makutu-Idofin dake ƙaramar hukumar Yagba East a jihar Kogi. Shaidu sun bayyanawa Aminiya cewa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin Litinin ne maharan suka sace Oba Shedrack Durojaye Obibeni da matarsa. Maharan masu ɗauke da muggan makamai sun kafa […]

Mahara sun sace basarake da matarsa a Kogi

Taswirar Jihar Kogi

Daga Tijani Labaran, Lokoja

Mahara sun sace wani basarake, Oba na Idofin da matarsa a hanyar Makutu-Idofin dake ƙaramar hukumar Yagba East a jihar Kogi.

Shaidu sun bayyanawa Aminiya cewa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin Litinin ne maharan suka sace Oba Shedrack Durojaye Obibeni da matarsa.

Maharan masu ɗauke da muggan makamai sun kafa shingen bincike a kan hanyar, inda suka yi awon gaba da basaraken da matarsa zuwa cikin daji.

Gwamnan Kogi ya kori Kwamishina da wasu 2 daga aiki

Bata-gari sun kone gidan rediyon Jihar Kogi

Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Kogi, SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace tuni ƴan sanda suka bi sahun maharan domin ceton basaraken da matarsa.

“A yanzu haka Jami’an ƴan sanda tare da  sauran hukumomin tsaro, da mafarauta na kan hanyar ceto su,” in ji Kakakin ƴan sandan.

Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja

MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP

Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas

Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo