Mahara sun sace mutum 50, sun sanya haraji a mahaifar mataimakin gwamnan Sakkwato
Maharan sun yi barazanar sake sace mutane a ƙauyen matuƙar ba a ba su harajin da suka sanya ba.
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Garin Idi da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka yi awon gaba da mutum sama da 50.
Ƙauyen shi ne mahaifar Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir.
- Matatar Dangote ta dawo sayar da fetur da Naira
- Trump ya jinjina wa Tinubu kan yaƙi da ta’addanci a Najeriya
Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun shiga garin ne tsakanin ƙarfe 10 na dare zuwa 12:30 na daren ranar Litinin.
Sun yi ta harbe-harbe domin firgita jama’a kafin su rabu gida biyu.
A cewar wani mazaunin garin, rukuni na farko ya shiga gidaje ya sace kusan mata 30, yayin da rukuni na biyu ya shiga wata makarantar allo ya yi garkuwa da almajirai manya da ƙanana sama da 20.
Kafin su tafi, ’yan bindigar sun saki mutum ɗaya domin ya kira mai gari, liman da sauran shugabannin al’umma domin tattaunawa.
Majiyar, ta ce a lokacin tattaunawar, maharan sun buƙaci a biya Naira miliyan ɗaya domin a saki matan, sannan Naira 600,000 domin sauran mutanen da suka kama.
Bayan haka, mutanen ƙauyen sun tattara Naira 600,000 suka bai wa ‘yan bindigar, inda nan take suka saki almajiran da suka kama.
Sai dai sun ce ba za su saki matan ba har sai an kawo Naira miliyan ɗaya cikin kwana biyu.
Mazauna ƙauyen sun kuma ce ‘yan bindigar sun sake dawowa a ranar Talata da misalin ƙarfe 7 na dare, inda suka tilasta wa ƙauyen biyan Naira 300,000 a matsayin haraji, tare da barazanar sake yin garkuwa da mutane idan ba a biya ba.
Sun ce saboda tsoron maharan, mutanen ƙauyen suka tattara kuɗin suka ba su, yayin da aka tilasta wa wasu mazauna ƙauyen haɗa sallar Magariba da Isha saboda lokacin da maharan suka shafe a cikin garin.
Mazauna Garin Idi, sun yi kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, suna mai cewa yawancin mutanen ƙauyen manoma ne kuma suna rayuwa cikin fargaba.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce rundunar ba ta da cikakken bayani kan lamarin.
Ya ce ba a kai musu rahoton faruwar harin ba daga yankin.